Jaridar Yaum Sabi ta buga a shafinta na yanar gizo cewa, jam'iyyar National Congress ta shugaba Umar Hassan Albashir ce ta gabatar da wannan shawara, kuma dukaknin mambobin majalisar dokokin kasar sun amince da hakan, daya daga cikin kusoshin jam'iyyar ta National Congress Abbas Khudr ya bayyana cewa halartar Sadiq Almahdi na da babban tasiri a siyasance wajen hada kan al'ummar Sudan, da kuma samun damar warware matsaloli da dama a bangaren siyasar kasar.
Kwanakin baya ne dai Sadiq Almahdi wanda shi ne shugaban kasar ta Sudan da ke ci a yanzu Umar Hassan Albashir ya yi wa juyin mulki, ya bayyana cewa Albashir yana wasa ne da hankulan alummar Sudan, lamarin da ya jawo ka ce na ce tsakaninsa da gwamnatin kasar. ABNA